Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Njeriya INEC ta ce mutanen da su ka yi rijista a halin yanzu sun kusa miliyan hudu.

Hakan na ƙunshe cikin alƙaluman da hukumar ke tattara wa wanda ta fitar a ranar Litinin.

Jihar Osun ce ke kan gaba a yawan mutanen da su ka yi rijistar wanda adadinsu ya kai 453,949.

Hukumar ta ce an kammala wa mutane 934,609 rijistar tare da ɗaukar dukkanin bayanansu ciki har da hoton yatsun su.

Hukumar ta ce maza ne mafi yawa daga cikin mutanen da su ka yi rijistar su 3,204,729 yayin da mata 2,735,838 su ka yi rijistar.

Daga cikin mutanen akwai wadanda su ka aika da bayanai don a yi musu gyara wasu kuwa su ka yi sabuwa da waɗanda tasu ta bata su ka aika da bayanai domin samun wata.

Haka kuma akwai masu buƙata ta musamman da tsofaffi duk a cikin mutanen da su ka yi rijistar.

Hukumar zaɓe INEC t fara rijistar ne tun a watan Yuni na shekarar 2021 da mu ke ciki.

Kimanin watanni biyar kenan aka fara rijistar, kuma ana kyauta zaton akwai sama da mutane miliyan 200 a Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: