Hukumar kashe gobara a jihar Kano ta yi nasarar ceto wasu mutane biyu da su ka jikkata bayan sun shiga rijiya don ceto wata akuya.

An ceto Malam Hassan mai shekaru 30, da Saddam Abdullahi mai shekaru 30 a duniya wadanda su ka shiga wata rijiya don ceto akuya a unguwar Kawon Mai Gari.
Mutanen biyu sun jikkata a ƙoƙarin su na ceto akuyar bayan sun shiga rijiyar wadda ke da ƙarancin ruwa a cikin ta.

Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar Saminu Yusif Abdullahi ya ce mutanen biyu sun yi koƙarin ceto wata akuya ne kuma a nan ne su ka jikkata bayan sun shiga rijiyar wadda ke da ƙarancin ruwa a cikin ta.

Ya ce al’amarin ya faru ne a unguwar Kawon Mai Gari a ranar Laraba da misalin ƙarfe biyar na yamma.
Tuni jami’an su ka garzata da mutanen zuwa asbitin ƙwararru na Murtala da ke birnin Kano domin ceto rayuwar su.