Shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya INEC reshen jihar Kano Farfesa Riskuwa Arabu Shehu ya buƙaci matasa da su jajirce tare da jurewa ƙalubalen rayuwa don zama wasu a nan gaba.
Farfesa Riskuwa ya bayyana haka ne a yayin taron yaye matasa 47 da aka koya wa sana’o’in dogaro da kai kyauta wanda aka yi a jiya Lahadi.
Farfesa Riskuwa wanda ya samu wakilcin babban akanta a hukumar Malam Hassan ya ce sai matasa sun yi amfani da lokacin su wajen aiki na gari kafin su zama wasu a rayuwa.
Riskuwa Arabu Shehu ya ƙara da cewa wannan ƙalubale ne ga matasa don ganin sun nemi na kan su ta hanyar dage wa domin ɗebe wa kan su takaici.
Taron da aka yi ranar Lahadi ya samu halartar muatne da dama ciki har da babban sakataren yada labaran gwamnan Kano Malam Abba Anwar.