Daga Amina Tahir Muhammad
Gwamnatin jihar Neja ta rushe gidan wani ƙasurgmin mai garkuwa da mutane.
Kwamishinan kananan hukumomi da harkokin tsaron cikin gida Emmanuel Umar, wanda ya sanya ido a kan rushe gidan ya ce wanda ake zargin ya fallasa cewa ya gina gidan ne da kudaden da ya samu daga ta’asar.
Gidan wanda ya kasance mai dauke da dakuna biu da wani bangareda ba a akamala ba yana a yankin Nkangbe a jihar.
Kwamishinan ya ce an dauki wannan matakin ne domin ya zama gargadi gasauran miyagun cewa gwamnatin jihar baza ta yarda masu laifi su mayyar da jihar mafakarsu ba.
Sai dai kuma kwamishinan yaki bayyar da cikakken bayani kan ko wanene mai garkuwa da mutanan da kuma yadda aka gano gidansa.
“wannan ginin mallakar wani mai garkuwa da mutane ne wanda aka kama” a cewar kwamishinan.