Rundunar sojin Najeriya ta ce ta hallaka mayakan Boko Haram da dama yayin da ta aike da dakarunta bayan da su ka mamaye yankin Bulguma ta jihar Borno.

Mai magana da yawun rundunar sojin ƙasa Onyema Nwachukwu ne ya sanar da haka bayan shafe awanni takwas a na musayar wuta da mayaƙan.

Mayaƙan sun kutsa kai cikin yankin da misalin ƙarfe tara na safiyar yau Asabar sannan su ka kashe sojoji ciki har da mai mukamin Birgediya Janar.

Kakakin ya ƙara da cewa har yanzu a na ci gaba da gwabza faɗan tsakanin su da mayakan Boko Haram a yankin.

An lalata makamai da dama mallakin mayaƙan Boko Haram tsageb ISWAP da kuma wasu motocin yaƙi a yayin faɗan.

Wannan ne hari mafi muni da aka kashe babban soji tun bayan da rundunar ke bayyana cewar mayakan Boko Haram na ajiye makamanci tare da kai kansu ga jami’an tsaro.

Leave a Reply

%d bloggers like this: