Rahotanni daga jihar Sokoto na tabbatar da mutuwar wasu mutane 14 yayin da yan bindiga su ka kai hari a karamar hukumar Sabon Birni ta jihar.
Hakan na zuwa ne awanni kadan bayan shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayar da umarni kara yawan jami’an tsaro don magance matsalar staro a jihar.
Yan bindiga sun kashe mutanen a kauyen Unguwan Lalle, Tsangerawa, da kauyen Tamindawa tare da raunata wasu da dama.
Sannan sun farwa matafiya tare da kashe wasu daga ciki har da direnban motar a yankin Gajid.
Wani bindike da jaridar Dailyy Trust ta yi ta gano adadin mutanen da aka kashe tsakanin ranakun Litinin da Talata sun kai 57.
Gwamnatin jihar ta tabbatar da mutuwar mutane 15 yayin da gwwamnan ke shirin gabatar da kasafin kudin shekarar 2022 a zauren majalisar jihar.


