Ƴan bindiga a jihar Katsina sun kashe ƴan sana biyu a yayin musayar wuta da su ka yi a wani daji da ke ƙaramar hukumar Safana.

Kwamishinan ƴan sandan a jihar Sanusi Buba ne ya sanar da haka a yayin gana wa da ƴan jarida a helkwatar ƴan sanda ta jihar.
Ya ce dakarun su sun yi yunƙurin kai farmaki ga ƴan bindigan da ke ɓoye a dajin Ɓaure a ƙarƙashin ƙaramar hukumar Safana.

Ƴan sandan sun kwato bindiga AK47 guda ɗaya da mashina da harsashi mai yawa .

Kwamishinan ya ce sun sami nasarar kashe yan bindiga biyu yayin musayar wutar da su ka yi a ranar Alhamis da daddare.
Kwamishinan ya tabbatar da cewar za su ci gaba da aiki tukuru don ganin sun kama ƴan bindigan tare da tabbatar da an hukumata su kamar yadda doka ta tanada.