Gwamnatin jihar Filato ta shirya don tinkarar barazanar ɓarkewar cutar Lasa da cutar amai da gudawa a jihar.

Kwamishinan lafiya a jihar Nimkong Ndam ne ya sanar da haka a yayin da yake gana wa da ƴan jarida a jihar.

Ta ce gwamnatin jihar ta aike da jami’an lafiyar jihar zuwa helkwatar hukumar daƙile cutuka masu yaduwa NCDC domin samun horo a kan yadda za su tafiyar da al’amuran mutanen da ke ɗauke da cutar.

Kwamishinan ya ƙara da cewa a yanayin sanyi su kan fuskanci ɓarkewar annobar cutar Lassa a jihar.

Ya ce mutane  a jihar na yawan amfani da namun daji musamman dangin ɓeraye wanda hakan ke silar ɓarkewar cutar.

Kuma yanayin sanyin na ɗauke da ƙura da iska wadda ka iya yaɗa cutuka da ke jikin dangogin namun dajin da ake iya ɗaukar cutar a jikin su musamman bayan an gasa su.

Kwamishinan y ace bayan mutanen da su ka tura sun kammala samun horo za su shirya horo ga ma’aikatan lafiya matakin farko domin su sami horo a kan yadda za su tafiyar da al’amuran masu cutar idan an samu.

Ma’aikatan lafiyar da za a bai wa horon a jihar sun shafi na dukkanin ƙananan hukumomi 17 na fadin jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: