Hukumar kashe gobara a jihar Kano ta ce an samu gawarwakin mutane 30 da su ka mutu a asakamakon kifewar wani jirgin ruwa a ƙaramar hukumar Ɓagwai.
Kakakin hukumar Saminu Yusif Abdullahi ne ya sanar da haka a wata snaarwa da ya raba wa manema labarai yau.
Ya ce a ranar da Talata an ceto mutane 20 yayin da aka ceto mutane 10 a ranar Laraba.
Sannan an cetow asu mutane bakwai da ran su sai kuma wasu mutane 12 da ake ci gaba da lalubawa a cikin ruwa.
Mafi yawa daga cikin mutanen da su ka mutu a sanadiyyar kifewar jirgin ruwan yara ne ƴan ƙasa da shekaru 20 a duniya.
Kakakin hukumar ya ce jami’an su haɗin gwiwa da masu sana’ar kamun kifi ne su ka kuɓutar da mutanen da aka samu.
Hukumar na jajanta wa a kan hatsarin jirgin ruwan wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 30 a Kano ranar Talata.