Rundunar ƴan sandan jihar Katsina ta kama wani da ake zargi da kai hari Ƴantumaki har su ka kashe dagacin garin.

An kama Yusif Abdullahi da sauran wasu mutane da ake zargi da hannun wajen kisan dagacin Ƴantumaki Alhaji Abubakar Atiku mai shekaru 55 a duniya..

Yayin da ya ke gabatar da masu laifin a gaban ƴan jarida, kwamishinan ƴan sandan jihar Sanusi Buba ya ce an aikata laifin ne tun a ranar 1 ga watan Yuni na shekarar 2020.

Ƴan sandan sun kama wanda ae zargin da muƙarraban sa a ranar 3 ga watan Disamban da mu ke ciki.

An gabatar da sauran masu laifi daban-daban a helkwatar ƴan sandan ciki har da ɓarayin motoci, ƴan fashi da makami da sauran masu aikata laifuka.

Sauran masu lafin da aka kama za a gurfanar da su a gaban kotu da zarar an kammala bincike a kan su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: