Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya bukashi shugaba Buhari ya ƙara ƙoƙarin da ya ke na yaki da yan bindiga a jihar.

Gwamnan ya bayyana haka ne yayin da ya karɓi tawagar jami’an staron da shugaban ƙasa ya aike jihar don duba halin tsaron da jihar ke ciki.

Hakan na zuwa ne bayan da shugaban ya sha suka daga al’ummar jihar na nuna halin ko in kula da mutanen yankin duk da mutanen da ake ta kashe wa a jihar.

Gwamna Tambuwal ya ce bayan ƙaddamar da dakarun Hadarin Daji a Zamfara yan bindiga sun matsa da kai hare-hare jihar Sokoto.

Ya ce yan bindigan na matsa wa da kai hare-hare ƙananan hukumomin Isa, Sabon Birni, Illela, da wasu yankunan da ke maoftaka da ƙananan hukumomin.

Gwamna Aminu Tambwal ya gabatar da wasu bayanai a kan halin rashin tsaron da ake ciki musamman a ƴan kwanakin nan.

Sannan ya koka a kan rashin isassun kayan aikkii ga jami’an staro wanda za su yaki yan bindigan da su ka addabi jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: