Daga Amina Tahir Muhammad Riskuwa

Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina ya ce akwai bukatar dukkan jihohin da ke Arewa maso Yamma su hada kai don magance matsalolin tsaro da suka addabi yankin.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke amsa tambayoyi daga manema labarai na fadar shugaban kasa bayan ya jagoranci tawagar dattawa jihar sa don ganawar sirri da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

A cewar Masari “Ina ganin abin da ya fi dacewa mu yi nasara wajen yakar wadannan ‘yan ta’adda shi ne mu duka jihohin mu, musamman Arewa maso Yamma.

“Amma idan wata jiha tana da manufa, wata kuma tana da wata manufa ta daban, to tabbas su (’yan bindiga) za su rika tafiya daga wannan jiha zuwa waccan. An yi sa’a, mun riga mun hada gwiwa da Jihohin da ke kan iyaka da mu, kamar Nasarawa da Neja, don kawo karshen matsalar.”
Dan gane da kisan da a kayi wa daya daga cikin kwamishinonin sa a baya-bayan nan Masari ya ce lamarin bashi da alaka da yan fashi ya na mai bayyana hakan a matsayin kisan gilla.
Gwamnan ya tabbatarwa da iyalan mamacin da ‘yan jihar cewa jami’an tsaro suna bakin kokarinsu wajen bankado musabbabin kisan.