Harin da ake kai wa jami’an hukumar kashe gobara idan sun je kashe gobara a Adamawa shi ne babban ƙalubalen da huukumar ke fuskanta a jihar a cewar kwamandan hukumar Philip Odu.
Hukumar kashe gobara a Najeriya reshen jihar Adamawa ta ce ta ceto rayukan mutane takwas tare da tseratar da dukiyar da ta haura biliyan uku.
Hukumar ta ce an samu iftila’in gobara a shekarar 2021 sau 64 a fadin jihar tun daga watan Janairun 2021 zuwa yanzu.
Kwamandan shiyya a hukumar Philip Odu ne ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN a Yola.
Ya ce sun kubutar da dukiyar da ta kai ƙimar kudi naira biliyan 3.8 a haɗɗuran gobarar da su ka faru a Adamawa.
Ya kara da cewa akwai wasu mutane uuku da aka tabbataer sun mutu a haɗduran gobarar da ta faru a jihar.
Philip Odu ya ce gobara ta laƙume dukiyar da ta kai naira milyan 290.60.
Daga cikin manyan ƙalubalen da su ke fuskanta akwai rashin hadin kan mutane wanda ya yi zargin a wasu lokutan mutane na kai wa jami’an su hari tare da lalata kayan aikin su.
Ya ƙara da cewa a mafi yawan lokuta sai an haɗa jami’an da za su ba su tsaro kafin zuwa domin kashe gobara a duk inda su ka samu kiran waya.
Shugaban ya bukaci mutane da su dinga ba su hadin kai domin cika ƙa’idar kafa hukumar na tseratar da rayuka da dukiyoyi.