Shekarun magen biyar a duniya kuma a ceto rayuwarta tare da miƙata wajen mai ita.

Hukumar kashe gobara a jihar Kano ta ceto wata mage da ta faɗa tsakanin wani gini a unguwar Yakasai a Kano.
Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar Saminu Yusif ne ya shaida hakan a yau Alhamis.

Ya ce jami’an su sun karɓi kiran ne a yammacin Laraba sannan su ka tashi zaratan jami’an domin ceto rayuwar magen wadda ta faɗa tsakanin ginin.

Jami’an sun yi aiki da basira wajen ceto rayuwar magen bayan sun halarci wajen ba tare da ɓata lokaci ba.
Saminu Yusif ya ce sun miƙa magen ga Hajiya Ta Annabi wadda ita ce mai ita.