Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana marigayi Alhaji Bashir Othman Tofa a matsayin ɗan kishin ƙasa.

A wata sanarwa da mai magan da yawunsa Malam Garba Shehu ya fitar, shugaba Buhari ya ce marigayin ya yi gwagwarmaya don ganin an smaar da ingantacciyar Najeriya.

Muhammadu Buhari ya tura tawaga domin ta’aziyyar marigayi Alhaji Bashir Tofa.

Daga cikin mutanen da aka aike akwai ministan tsaro, da ministan ruwa sai mai magana da yawun sa Malam Garba Shehu.

Haka kuma shugaban ya aike da saƙon ta’aziyyar sa ga al’ummar jihar Kano da ma Najeriya a bisa babban rashin da aka yi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: