Gwamnan ya ce sai an sauya salo tare da ɗaukar matakin ƙone dazukan arewa hakan ne kaɗai zai kawo ƙarshen ƴan bindigan.

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El’rufa’i ya ce ƙone dazukan arewacin ƙasar ne kaɗai zai kawo ƙarsehn ƴan bindigan da su ka addabi yankunan.
Gwamnan ya b ayyana haka ne a yayin tattaunawarsa da gidan talabiji na Arise TV.

Ya ce tinkarar ƴan bindiga ta sama da ƙasa a dukkanin jihohin arewa maso yamma ne zai iya kawo ƙarshen lamarin duk da cewar hakan zai shafi waɗanda ba su ji ba su gani ba.

Ya ƙara da cewa kawo ƙarshen ƴan bindiga ne zai bai wa manoma damar komawa gonakinsu domin ci gaba da noma a yankin arewa.