Hukumar kashe gobara ta ce wasu mutane biyu sun rasa ran su a sanadiyyar wata gobara data tashi a wani gida da ke kan hanyar zuwa Gwarzo.

Zainab Yusha’u da ɗan mai shekaru 25 a duniya da ɗan ta Sulaiman Usaini mai shekara ɗaya sun rasa ran su yayin da gobarar ta cimmusu.
Lamarin ya faru a safiyar yau kuma hukumar ta samu nasarar kashe gobarar.

Hukumar ta ja hankalin mutane da su ƙara kula da al’amuran wuta musamman a wannan lokaci na sanyi domin hana afkuwar tashin gobara.

A wani labarin kuma hukumar kashe gobara a jihar Kano ta gano gawar wani mutum mai kimanin shekaru 50 a duniya.
Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar Saminu Yusif ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai.
Ya ce sun samu kiran waya daga wani Jamilu Harisu wanda ya sanar da su sun ga wani mutum a bakin wani ruwa a unguwar Sallari.
Jami’an sun isa wajen a yau bayan karɓar kiran da su ka yi sannan su ka iske mutumin yashe a gefen ruwan.
Saminu Yusif ya ce bayan riskar mutumin daga bisani aka tabbatar ya mutu.
Tuni hukumar kashe gobara ta Kano ta miƙa gawar mamacin ga baturen ƴan sanda na Filin Hokey domin faɗaɗa bincike.
Har lokacin da mu ke kammala wannan labari ba mu ji bayani daga jami’an tsaron a kan musabbabin mutuwar mutumin ba.