Gwamnan jihar Zamfara Muhammad Bello Matawalle ya ce gwamnatin jihar za ta samar da jiragen yaki na zamani samfurin Tucano domin yaƙi a yan bindiga.

Gwamnan ya bayyana haka ne yayin da yake bayani a dangane da hare-haren da aka kai wasu kauyuka 10 da ke karƙashin ƙananan hukumomin Anka da Bukkuyum.
Muhammad Matawalle ya ce za a kai jiragen yaƙin ne daga ƙasar Amurka ba da jima wa ba.

A sakamakon hare-haren mutane da dama sun yi gudun hijira zuwa wasu ƙauyuka domin tseratar da rayuwarsu.

Gwamnan ya ce ayyana ƴan bindiga a matsayin ƴan ta’adda da shugaban Najeriya ya yi zai taimaka wajen yhakarsu tare da kawar da su baki ɗaya.
Matawalle ya bayyana haka a yau yayin da ya ziyarci sabbin sojojin da aka ɗauka a kananan hukumomi 14 na faɗin jihar.
Gwamnan ya ce sun fara shawarar yadda za a yaki yan bindiga da jirgin da za a kai daga ƙasar Amurka kuma tattauuna wa ta yi nisa wadda ta kunshi kwamishinan tsaro da sauran masu ruwa da tsaki a al’amuran tsaron jihar.
An shafe tsawon lokuta ana fama da hare-haren ƴan bindiga a jihar Zamfara wanda hakan ya yi silar salwantar da rayuwakan jama’a da dama.