Rundunar ƴan sandan jihar Kwara ta musanta raɗe-raɗin da ake kan cewar wasu ƴan bindiga masu goyon bayan Bello turji na koma wa wasu dazukan jihar.

Mai magana da yawun ƴan sandan jihar SP. Ajayi Okasanmi ne ya sanar da haka yau a Ilorin babban birnin jihar.
Rundunar ta ce sam babu cikakkaen bayani a dangane da rahoton da ake yada wa na komawar yaran Bello turji zuwa wasu tazukan jihar domin samun mafaka.

Ya ce rundunar yan sandan jihar hadin gwiwa da jami’an sojin ƙasar sun tsaurara mattakan tsaro a dukkanin yankunan jihar domin smaar da tsaro.

Sannan kwamishinan yan sandan jihar ya bayar da umarni ga jami’an sa domin gudanar na sintiri na tsawon awanni 24 a dukkanin hanyoyin shirge da fice na jihar.
Sannan ya buƙaci al’ummar garin da su kai rahoton dukkanin wani wanda su ka gani baƙo kuma ba su gamsu da shi ba.