Gwamnatin jihar Borno ta tabbatar da kafa wani kwamitin mutane biyar da zai bi diddigin kisan wani ɗalibi a jihar.

Ma’aikatar ilimi a jihar ce ta ce ta kafa wani kwamiti mai mutum 5 da zai binciki lamarin da ya kai ga yanke  makogoro ga wani ɗalibin makarantar El-Kanemi Islamic Theology da ke Maiduguri.

An hallaka ɗalibin mai suna Jibril Sadi Mato ta hanyar yanke maƙogaronsa.

A wata wasika da ya aikewa shugaban kwamitin wanda shi ne sakataren ma’aikatar Ilimi Alhaji Sadiq Kadafur mai dauke da sa hannun babban sakataren ma’aikatar Muhammad Mustapha Abatcha ya umarci kwamitin da ya gudanar da bincike tare da kai ga gano musabbabin faruwar lamarin .

Kwamitin wanda ya hada da wakilin kwamishinan yan sanda wakilin DSS, wakilin kwamandan hukumar kare fararen hula  da kuma daraktar tabbatar da ingancin ma’aikatar ilimi Hajiya Hadiza Nasiru Wali.

A na sa ran kwamitin zai mika rahotonsa  cikin mako guda.

Rahotanni sun nuna  cewa a ranar Juma’a  jami’an yan sandan jihar Borno sun kama Umar Goni dalibin babbar sakandire bisa zargin sa da aikata laifin.

An ce Goni ya yi amfani da reza ne wajen tsaga makogoron Jibrin Sadi Ramadan matashin abokin aikinsa bayan wata yar rashin jituwa da ta faru tsakaninsu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: