Daga Amina Tahir Muhammad

Gwamnatin tarayya a wani yunkuri na kawo karshen cutar ƙanjamau a matsayin barazana ga lafiyar al’umma, ta bayyana shirin kashe N62bn a duk shekara domin kula da masu dauke da cutar kanjamau. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi wannan alƙawarin ne a ranar Talata a lokacin da yake ƙaddamar da asusun tallafawa masu cutar ƙanjamau na Najeriya naira biliyan 62.
Shugaba Buhari ya sha alwashin gwamnatinsa za ta ci gaba da ba da fifiko ga ayyukan kiwon lafiya don magance cututtuka masu kashe mutane da kuma matsalolin lafiyar jama’a.

Shugaba Buhari, a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Femi Adesina, ya fitar, ya ce manufar hadin gwiwar Najeriya da kamfanoni masu zaman kansu don magance cutar ta Korona ya samar da ƙofofin samar da kudade don yin amfani da su don ci gaba da yaki da cutar kanjamau.

Sanarwar ta ƙara da cewa, “A taron koli na Majalisar Dinkin Duniya da ya gabata kan cutar kanjamau, na yi kira da a sake ,daukar matakan da suka dace don magance cutar kanjamau a Afirka.
”Kawo karshen cutar kanjamau a matsayin barazana ga lafiyar al’umma a Najeriya zai bukaci karin kudaden cikin gida. Mun ci gaba da yin kyakkyawan alƙawarin sanya ƙarin mutane masu fama da cutar kanjamau a kan jiyya kowace shekara ta amfani da albarkatun ƙasa.
Shugaba Buhari ya yabawa hukumar yaki da cutar kanjamau ta ƙasa hadin gwiwar ‘yan kasuwan Najeriya da ke yaki da cutar kanjamau a kan kokarin da suka yi na samar da asusun kula da masu cutar kanjamau a Najeriya domin samar da jariran da ba su da cutar.
Ya kuma bayyana jin dadinsa da halartar manyan mutane masu ruwa da tsaki domin yaki da cutar kanjamau a duniya.
A nasa jawabin, sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ya bayyana cewa tun shekarar 2005 an kashe kimanin dala biliyan 6.2 wajen yaki da cutar kanjamau a Najeriya.