Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sha alwashin samar da sauyi a cikin watanni masu zuwa.

Shugaban ya tabbatar da hakan yayin da ya ke ƙaddamar da kwamitin da zai duba aikin mayar da ƴan gudun hijira muhallinsu.

Muhammadu Buhar ya ce jami’an tsaro za su sauya salon yaƙi da ƴan ta’adda musamman a arewa maso gabashin ƙasar.

A wani rahoto da hukumar SBM Intelligence ta gabatar a jiya, ta tabbatar da cewar an hllaka mutane 10,266 a Najeriya cikin shekarar 2021.

Shugaba Buhari ya ce gwamnatin sa za ta tabbatar da ci gaba da mayar da hankali wajen samar da zaman lafiya domin ci gaba a ƙasar.

Haka kuma ya ce za su tabbatar sun bai wa matasa masu tasowa kula wa ta musaman kasancewar su manyan gobe a  ƙasar.

Muhammadu Buhari ya ce kwamitin da aka samar ana sa ran zai gabatar da tsare-tsaren sa na shekaru uku a nan gaba, sa’annan za a dinga gabatar da ci gaban da aka samu duk bayan watanni uku wanda za su fara gabatar da na farko a farkon makon watan Maris.

Kwamitin da aka kafa ya ƙunshi manyan shugabannin tsaro da masu bai wa shugaban shawara  a kan tsaro da kuma ministar jin ƙai da ministar kasafi da tsare-tsare, minsitan tsaro ministan harkokin cikin gida da inistan harkokin ƙasashen waje.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: