Minstan ilimi a Najeriya Malam Adamu Adamu ya ce kundin tsarin mulkin Najeriya ya bayar da dama ga muaulmi su sanya hijabi a makarantu.

Ministan na wannan jawabi ne a yayin da ya halarci wani taro da mata muaulmi su ka shirya don ɗabbaƙa ranar hijabi ta duniya.
Malam Adamu Adamu wanda Hajiya Sidiƙat ta wakilce shi a wajen taron, ya ce abin takaici ne ganin yadda wasu ke sukan hakan a cikin kasar.

Ya ce kundin tsarin mulki ya bayar da dama ga yan ƙasa domin bin duk addinin da su ke so tare da bin tsarin da ke cikin sa.

Ya ƙara da cewa saka hijabi koyarwar addinin musulunci ce wanda ya zo cikin sunnan manzon Allah S.A.W.
Minstan ya ce abin takaci ne a kan irin sabanin da ake samu musamman a jihar Kwara wanda aka hana sanya hijabi a wata makaranta lamarin da ya haifar da zanga-zanga har aka rasa ran mutum guda cikin ɗaliban makarantar.
Mahukunta a makarantar Baptist High School sun nuna rashin goyon bayan saka hijabi a makarantar su wanda ƙungiyar kiristoci ta CAN ta goyi bayan su a kai.
Musulmi a jihar Kwara musamman na makarantar na kallon hakan a matsayin cin fuska tare da tauye musu wata dama da kundin taarin mulki ya basu har hakan ya sa su ka fita zanga-zanga a ranar Alhamis domin nuna rashin jin daɗinsu a dangane da matakin da hukumar makarantar ta ɗauka.