Hukumar hana yaduwar cutuka masu yaduwa a Najeriya NCDC ta ce mutane 40 ne su ka rasa rayukansu a sakamakon cutar Lassa a watan Janairun da ya gabata.

A rahoton halin da ake ciki a dangane da ctar wanda hukumar ta saba fitarwa, hukumar ta ce an samu ƙaruwar mutuwar mutane da kashi 22.2 cikin ɗari.

Rahoton ya tabbatar da cewar akwai wasu mutane 211 da aka tabbatar su na ɗauke da cutar Lassa yayin da ake zargin mutane 981 sun kamu da cutar.

Kashi 80 cikin ɗari na mutanen da aka tabbatar su na ɗauke da cutar sun fito ne daga jihohin Edo, Bauchi, da jihar Ondo.

Hukumar NCDC ta ce an samu masu ɗauke da cutar a jihohi 14 na Najeriya.

Sai dai hukumar ta ce a rahoton da ta tatara na watan Janairun shekarar da mu ke ciki babu wani ma’aikacin lafiya da ya kamu da cutar.

Sa’annan dukkanin hukumomin da aka tanada don yaki da cutar na aiki tuƙuru don ganin an kawo ƙarshenta baki ɗaya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: