Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sauka a Abuja bayan dawowarsa daga ƙasar Habasha wanda ya ya halarci wani taro a ƙarshen makon da ya gabata.

A yau Litinin shugaban ya dawo Najeriya bayan da ya gana da mataimakiyar  babbar sakatare a majalisar ɗinkin duniya Amina Mohammed.

Shugaban ya gana da wasu mukarrabai a majalisar ɗinkin duniya bayan da ya halarci taron ƙungiyar tarayyar Afrika a Adis Ababa na ƙasar Habasha.

A yayin taron da ya halarta na haɗaɗɗiyar ƙungiyar tarayyar Afrika AU a Addis Ababa, shugaba Buhari ya sha alwashin ci gaba da bayar da goyon baya wajen wanzuwar zaman lafiya.

Haka kuma shugaban ya ce gwamnati za ta tabbatar an ci gaba da byƙasa shirin bayar da tallafi domin kawar da talauci a cikin al’umma.

Shugaba Buhari a yayin taron da ya halarta ya samu rakiyar wasu daga cikin muƙarraban gwamnatin sa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: