Gwamnatin jihar Neja ta sanya wani lada da za ta dinga bayarwa ga masu tsegunta mata bayanai a kan ƴan bindigan da su ka addabi jihar.

Babbar sakatariyar yaɗa labaran gwamnan jihar Mary Noel-Berje ce ta sanar da hakan a yau Asabar.
Ta ce an ɗauki matakin hakan ne ganin yadda ƴan bindiga su ka matsa da kai hare-hare a kwanakin nan.

Ta ƙara da cewa gwamnan jihar Abubakar Sani Bello ya samar da wani ɗaki na musamman ga jami’an tsaro domin aike da bayanan sirri a kan ƴan bindiga.

Sai dai ba ta bayyana kuɗin da za a dinga bai wa mutanen da su ka tsegunta wa jami’an tsaro halin da ƴan bindiga ke ciki ba.
Jihar Neja na daga cikin jihohin da ƴan bindiga su ka matsa da kai hare-hare wanda har ta kai ana yin garkuwa da ɗalibai domin karɓar kudin fansa.