Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El’rufa’i ya bayyana cewar rashin tsaron da ake fama da shi a halin yanzu ya zarce taɓarɓarewar tsaro a lokacin da mayaƙan Boko Haram ke yawan kai hare-hare.
Gwamnan ya ce yawa kashe jama’a da ake yi ya zarce mutanen da aka kashe a yayin da mayaƙan Boko Haram ke yawan kai hare-hare.
Malam Nasir El’rufa’i ya bayyana haka ne a Abuja yau Alhamis bayan yayin da ya ke bayar da rahoto a kan sha’anin tsaro wanda kwamitin sadarwa na fadar shugaban ƙasa su ke gudanarwa a kowanne mako.
Gwamnan ya yi zargi hakan da irin makaman da ƴan bindiga su ke riƙewa ya zarce na jami’an staron ƙasar.
Sannan ya ce mafi yawan jihohin da ayyukan ƴan bindiga su ke ta’azzara sun zarce ta’addancin mayaƙan Boko Haram a jihohin Zamfara, Kaduna, Neja, Sokoto Kebbi da da Katsina.
Gwamna El’rufa’i ya ce gwamnatinsa za ta tabbatar ta samar da na’u’rori na zamani kamar kyamarorin tsaro domin tabbaar da tsaro a ciki da wajen jihar kafin ƙarshen shekarar 2022 da mu ke ciki.