Hukumar lura da dakile cutyka masu yaɗuwa a Najeriya NCDC ta ce mutane dubu uku ne su ka rasa rayukansu a sanadiyyar cutar Korona.
A wata sanarwa da hukumar ta fita, ta ce sama da mutane dubu ɗari biyu aka samu sun kamu da cutar, sai dai fiye da kashi 80 cikin 100 sun warke kuma an sallamesu.
Hukumar ta ce ta samu wasu darrusa na dakile cutuka masu yaɗuwa tun bayan ɓullar annobar Korona da cutar Lassa.
Sai dai a wannan lokaci hukumar ta mayar da hankali ne a kan cutukan Lassa da cutar amai da gudawa wato Kwalara wadda ke ci gaba da yaɗuwa a wasu jihohin Najeriya.
A ranar 27 ga watan Fabrarun da ya gabata ne dai aka cika shekaru biyu cif da ɓullar cutar Korona a Najeriya wadda ta yi sanadiyyar rasa rayuwar mutane dubu uku a faɗin ƙasar.