Shugaban kamfanin mai a Najeriya Malam Mele Kyari ya ce ƴan Najeriya su dinga siyan man fetur ɗin da su ke da buƙatar sa a kowacce rana domin rage cunkoso a gidajen mai a Najeriya.

Shugaban ya bayyana haka ne wanda ya yi zargin siyan man da mutane ke yi da yawa na da alaƙa da cunkoson dogayen layi da ake fama da shi a ƙasar.
Kamfanin mai a Najeriya NNPC ya ce nan da wani kanƙanin lokaci zai samar da wadataccen man fetur da ya haura lita biliyan 1.7.

Kamfanin ya ce zai raba man fetur ɗin ga gidajen mai daban-daban na Najeriya domin rage wahalar man da ake fuskanta a faɗin ƙasar.

Shugaban kamfanin Meke Kyari ne ya bayyana haka yayin da ya tarbi shugabannin ƙungoyoyin masu gidajen mai da dillalan man fetur da kuma ma’aikatan gidajen mai a Abuja.
Ya ce malam Mele Kyari ya ce ya lura da ƙaramcin man da ake fuskanta a ƙasar wanda hakan ya haifar da cunkoso a gidajen mai da aka samu su na bayar wa.