Tsohon shugaban hukumar zaɓe a Najeriya Fafesa Attahiru Jega y ace tsarin shugabancin da ke tafiya a Najeriya hanya ce da ƙasar ta kama wajen rugujewarta.

Farfesa Jega ya bayyana haka ne ranar Laraba a Abuja yayin wani taron da ƙungiyar ƙwadago a Najeriya ta shirya.

Jega ya ce tsarin mulkin da ake gudanarwa a Najeriya a yanzu tamkar ana tafiya ne a makance domin babu hanyar da aka nufa ta gyara illa taɓarɓarewar tsarin shugabancin.

Taron da aka shirya domin duba makomar tsarin shugabancin da ake gudanarwa a halin yanzu da kuma zaɓen da aka tinkara na shekarar 2023, Jega ya ce tattalin arziƙi a halin yanzu ya yi rauni a ƙasar kuma duk hakan na da alaƙa da rashin kyakkyawan shugabanci na gari.

Sannan ya ce tsarin shugabancin ba zai ci gaba ba har sai an samar da haɗin kai a tsakanin ma’aikata tare da fitar da manufa mai kyau wanda ya ce hakan zai taimaka wajen samar da nasara domin magance matsalolin da ake fusknata a ƙasar a halin yanzu.

Jega ya bayyana yadda ake samun koma baya a wajen walwalar jama’a, tsaro da tattalin arziƙin ƙasa wanda hakan ya zamto babban ƙalubale da ake fusknata  a halin yanzu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: