Mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya shiga jerin masu neman kujerar shugabancin kasar Najeriy a shekarar 2023.

Mataimaikin shugaban ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 2023 domin ɗorawa daga inda gwamnatin shugaba Buhari ta tsaya.
Ya ce ya na da sha’awar ɗorawa d shugabancin ne domin inganta rayuwar al’ummar ƙasar bisa ƙwarewar da ya samu a mulki.

Sannan ya samu ganawa da manyan ƴan kasuwa da talakawa da masu sana’ar wasan kaikwayo na kudanci da arewacin kasar.

Farfesa Yemi Osinbajo ya buɗe ofishin yaƙin neman zaɓensa da ke Wuse a babban birnin tarayya buja.
Mutane a jam’iyyu daban-daban na nuna sha’awar stayawa takarar shugabancin a matakai daban-daban tun bayan da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa INEC ta ɗage takunkumi domin ayyana aniyar tsayawa takara da kuma bayar da damar siyar da fom ga masu sha’awar neman kujeru a mataki daban-daban.