Wata babbar Kotun jihar Ogun ta ba da umarnin tsare mataimakin Sufeta Janar na ƴan sanda, hedkwatar shiyya ta 2, Onikan, jihar Legas da kuma Sufurtanda, Tijani Taofiq, bisa raina Kotu.

Manyan jami’an ƴan sandan sun yi watsi da umarnin kotu wanda ya buƙaci AIG ya biya N500,000 yayin da Sufurtanda Taofiq zai biya N50,000 na diyyar ɓata sunan da suka yi wa wani ɗan China, Chen Zheng.
Ana zargin jami’an ƴan sandan bisa damƙe ɗan China kan zargin aikata babban laifi kuma daga bisani suka kwace Fasfo ɗinsa.

A ranar 9 ga watan Mayu, Alƙali Olugboyega Ogunfowora na babbar Kotun Ogun, ya umarci a saki Fasfon ɗan China mai lamba No.EB4555829.

Ogunfowora ya yi gargaɗin cewa rashin bin umarnin Kotu na sakin Fasfon da kuma biyan tarar da aka wa Jami’an raini ne kuma laifi ne da ke ƙunshe da hukunci a kundin mulkin ƙasa.
A bisa haka Mai Shari’a Olugboyega ya umarci a tsare jami’an a gidan yarin Ibara da ke Abeokuta har sai kayyakin ɗan Chana sun dawo.
Da yake zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan zaman Kotun, Lauyan wanda ya shigar da ƙara, Seun Akinbiyi, SAN, ya yaba da furucin Kotu.
Lauya Akinbiyi ya ƙara da cewa irin wannan hukuncin zai sa mutane su amince cewa ɓangaren shari’ar ƙasar nan shi ne gatan mutumin da be da kowa.
Ya kuma bayyana cewa:
“Da izinin Allah zamu zuba ido mu ga yadda za’a aiwatar da umarnin Kotu, wannan ɗaurin da Kotu ta yi wa AIG da Sufurtanda, zamu ga yadda zai karkare.”