Wasu matasa a jihar Sokoto sun yi sanadiyyar mutuwar wata ɗaliba bisa zargin ɓatanci ga fiyayyen halitta annabi Muhammad S.A.W.

Matasan sun ƙone ɗalibar da ranta a yau Alhamis bayan zargin da ake na yin ɓatanci ga Annai Muhammad S.A.W.

ɗalibar na yin karatu ne a makarantar kwalejin ilimi ta Shehu Shagari a jihar.

Rahotanni sun tabbatar da cewar sai da matasan su ka daki ɗalibar kafin daga bisani su ka yi amfani da taya wajen ƙone ta.

Tuni gwamnatin jihar ta bayar da umarnin rufe makarantar tare da kafa kwamiti domin gudanar da bincike a kai.

Kwamishinan yaɗa labarai a jihar Isa Bajini Galadanchi ya ce gwamnan jihar ya bai wa hukumar kula da manyan makarantu umarnin tsara yadda z aa gudanar da binckke a kan lamarin.

Tuni aka aike da jami’an tsaro makarantar domin daƙile wata hatsaniya da ka iya faruwa a gaba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: