Kwamitin zartarwa, NEC, na jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ta yanke shawarar bawa kowa fitowa takarar shugaban ƙasa a maimakon mika mulkin ga yanki guda na ƙasar.

Kwamitin zartarwa na jam’iyyar PDP, ta yi watsi da tsarin karɓa-karɓa ta ce kowa zai iya neman takarar shugaban ƙasa.
Jam’iyyar ta kuma tabbatar da cewa za ta yi taronta na ƙasa a babban birnin tarayya, Abuja a ƙarshen watan Mayun 2022.

Mai magana da yawun PDP, Debo Ologunaba, ya bayyana hakan yayin da ya ke yi wa manema labarai jawabi a sakatariyar jam’iyyar a Abuja.

Kwamitin mai jagorancin Gwamna Samuel Ortom na Jihar Benue ne ya bada shawarar cewa duk da cewa karɓa-karɓa na kundin tsarin jam’iyyar, a jingine shi a babban zaɓen 2023.
Da ya ke magana kafin zaɓen na NEC, Dr Iyorchia Ayu, shugaban jam’iyar na ƙasa, ya ce NEC din tana aiki tare da rana don daidaita jam’iyyar.
Yayi bayani kamar haka:
“Muna kan aiki domin babban taron mu na ƙasa, kuma za mu yi muku bayani a nan gaba.
Muna son mu miƙa godiya da waɗanda suka yi aiki, a kwamitoci daban-daban.
“Yanayin jam’iyyar ya fara canja wa, kowa na aiki tuƙuru kuma idan muka cigaba a haka babu abin da zai hana mu kwace mulki daga jam’iyyar APC.
“Shugaban ƙungiyar gwamnonin PDP kuma Gwamnan Sokoto Aminu Tambuwal ya ce yanzu ma aka fara yi wa jam’iyyar garambawul kuma ‘muna tare da kai har zuwa zaɓe na ƙasa.”