Hukumar yaƙi da rashawa da cin hanci EFCC, ta kama tsohuwar Shugabar Majalisar Wakilan ƙasar, Ms Patricia Etteh.

Rahotanni daga kafafen sadarwa da dama sun ruwaito cewa EFCC ta yi cafke Ms Etteh kan zargin almundahanar kuɗaɗe a ma’aikatar raya yankin Neja Delta wato NDDC da yawansu ya kai naira miliyan 287.

Wata majiyar EFCC ta fada wa jaridar Punch cewa Ms Etteh ta karɓi naira miliyan 130 daga kamfanin Phil Jin Project Limited da NDDC ta bai wa kwangilar naira miliyan 240 a 2011.

A kan haka a yanzu EFCC ta neme ta ta yi bayanin shigar kuɗin asusunta amma ta gaza fadar komai a kai.

Ita kaɗai ce mata a tarihin Najeriya da aka taɓa zaɓa kakakin majalisar tarayya.

An zaɓi Patricia Etteh a matsayin Shugabar Majalisar Wakilai a 2007, to amma ta yi murabus ne bayan ƴan watanni bisa zargin karkatar da wasu kuɗaɗe.

Ƴan majalisa a lokacin sun yi barazanar tsige ta daga mukamin Shugabar Majalisar kafin ta yanke shawarar sauka da kanta.

A wancan lokacin ana zarginta da ware wasu maƙudan kuɗaɗe don bada kwangilar gyaran gidan da aka tanadar wa kakakin majalisa.

‘Etteh ba darakta bace ko ƴar kwangila, saboda haka me ya kai wannan kuɗi asusunta.

Akan haka muke bukatar ta yi bayani kuma kawo yanzu bata yi ba,” in ji majiyar.

Idan baku manta ba kwanaki kaɗan mun kawo maku rahotan
Cewa EFCC ta cafke Akanta Janar na ƙasar, Ahmed Idris, bisa zargin sama da faɗi da Naira biliyan 80.

EFCC ta ce ta kama shi ne bayan ya ki amsa gayyatar da ta yi masa don amsa tambayoyi.

Lamarin dayaja cecekuce a kafafen sadarwa kan kama Akanta Janar ɗin da zargin wawushe biliyoyin, la’akari da cewa yana riƙe da babbar kujera a gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da ke iƙirarin yaƙi da cin hanci da rashawa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: