Wata babbar kotun jihar Legas a ranar Juma’a, ta yanke hukuncin kisa kan wani bature ɗan kasar Denmark, Dane Peter Nielsen, bisa laifin kashe matarsa ƴar Najeriya da diyarsa.

Alkali Bolanle Okikiolu-Ighile ya yankewa Dane hukuncin kisan ta hanyar rataya ne sakamakon shari’ar da akayi wanda gwamnatin jihar Legas ta shigar a kansa.
An tuhumi Dane da laifin kashe matarsa mai suna Zainab, da ɗiyarsu ƴar shekara uku mai suna Petra, a jihar Legas.

Gwamnatin jihar tace Dane ya hallaka Zainab da Petra ne misalin karfe 3:45 na dare cikin gida mai lamba No. 4, Flat 17, Bella Vista Tower, Banana Island, Ikoyi, jihar Lagos.

An gurfanar da Dane Peter a ranar 13 ga Yuni, 2018.