Magoya bayan ɗan takaran kujerar shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Tinubu, sun buƙaci ya zaɓi Gwamna Abdullahi Ganduje matsayin mataimakinsa inda ya lashe zaɓen fidda gwani.

Ɗaruruwan masoyan da suka tarɓi ɗan takarar a tashar jirgin sama na Mallam Aminu Kano, suna yi ihun “Najeriya sai Bola Tinubu tare da Ganduje matsayin mataimakin shugaban ƙasa.”

Tinubu ya kai ziyara jihar Kano ne domin ganawa da deleget ɗin jam’iyyar don neman goyon bayansu a zaɓen fidda gwanin ɗan takaran shugaban kasa.

Gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, shi ne ya jagoranci tawagar shugabannin jam’iyya zuwa wurin tarbar ɗan takarar shugaban ƙasa.

Tinubu jagora ne a jam’iyyar All Progressives Congress, kuma tsohon gwamnan jihar Legas

Za’a gudanar da zaɓen fidda gwanin ranar 29 ga Mayu, a farfajiyar Eagle Square dake Abuja.

Leave a Reply

%d bloggers like this: