Gwamnan Jihar Ondo Rotimi Akeredola ya dakatar da gudunar da bikin ranar Dimokradiyya a fadin Jihar.

Gwamnan Jihar Rotimi Akeredola shine wanda ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter a yau Asabar.
Gwamnan ya bayyana cewa sun soke gudunar da bikin ne sakamakon hallaka mutane da aka yi a wata coci a Jihar a ranar Lahadi.

Rotimi ya ce sun yi hakan ne domin nuna girmamawa ga mutanen da ‘yan bindigan su ka hallaka,da kuma bada dama ga ‘yan Jihar su yi zaman makokin mutanen da ‘yan bindigan su ka hallaka.

Yan bindigan sun kai hari ne a farkon watan Yuni kuma su ka hallaka mutane 40 tare da jikkata wasu.
Gwamnatin tarayya ta ce a binciken da ta gudanar ta gano mayakan ISWAP ne su ka kai hari a cocin.