Tsohon gwamnan Jihar Kano kuma dan takarar jam’iyyar NNPP Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso yayi wata ganawa da dan takarar shugaba kasa a jam’iyyar Labour Party wato Peter Obi a yau Asabar.
Sanata Rabi’u Kwankwaso ya bayyana hakan a yayin hirar da ya yi BBC a yau Asabar.
Kwankwaso ya bayyana cewa akwai yuwuwar su cure guri guda a yayin zaben shekarar 2023 mai zuwa.
A yayin tattaunawa da BBC an tambayi Sanata Kwankwaso cewa waye zai kasance a matsayin shgaban kasa da mataimaki shi da Peter Obi.
Sai kwankwaso ya bayyana cewa daga lokacin da su ka kammala tattaunawa wanda ya kasance a matsayin shine babba to shi za a tsayar a matsayin shugaban wanda kuma ya kasance karami sai a bashi mataimaki.
Tun daga lokacin da Kwankwaso da Peter Obi su ka bayyana aniyar su ta tsayawa takarar sun samu goyan bayan daga gurare daban-daban na fadin Najeriya.