Hukumar bayar da agajin gaggawa ta NEMA a ranar Alhamis ta karbi ‘yan Najeriya 98 da suka makale a garin Agadez na Jamhuriyar Nijar.

Shugaban hukumar NEMA reshen jihar Kano Dr Nuradeen Abdullahi ne ya bayyana hakan a lokacin da yake karbar wadanda suka koma Kano.

Abdullahi ya ce an mayar da wadanda suka koma Kano ne a cikin motocin alfarma guda uku da ke karkashin kulawar Hukumar Kula ƴan gudun Hijira ta Duniya (IOM) daga Agadez.

Ya ce wadanda aka mayar da su sun hada da manya maza 81, manyan mata shida da yara 11 mata uku da maza takwas.

Ya ce wadanda suka koma daga sassa daban-daban na Najeriya da suka hada da Kano da Kaduna da Katsina da kuma jihar Edo.

Ya ƙara da cewa wadanda aka mayar da su za a horar da su na tsawon kwanaki hudu don dogaro da kansu kuma za a ba su tallafi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: