Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake tabbatar da cewar gwamnatinsa ta bai wa hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya INEC cikakken goyon baya domin gudanar da zabe cikin na gaskiya da adalci a shekarar 2023.

Shugaban ya kuma baiwa INEC tabbacin samun ‘yancin kai, yana mai cewa bayan kammala zaben fidda gwani na jam’iyyun siyasa, yanzu idanunsu sun karkata ga zaben shekarar 2023 a Najeriya.
Shugaba Buhari, a cewar wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Garba Shehu, ya fitar a daren Laraba, ya ce shugaban ya bayyana haka ne yayin wani taro da wakilan ‘yan Najeriya mazauna kasar Portugal.

Ya ce suna kuma sa ran samun nasarar mika mulki ga gwamnati mai zuwa, Kamar yadda ya sha fada a baya, gwamnatinsu ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen yin abubuwan da suka dace da kuma jin dadin ‘yan Najeriya na gida da waje.

Buhari wanda ya ba da misali da zabukan gwamnoni da aka gudanar a jihohin Anambra da Ekiti, ya ce gwamnatinsa za ta tabbatar da cewa ba ta da hurumin yin katsalandan a zabe tare da dagewa cewa a bar ‘yan Najeriya su zabi jam’iyya da dan takarar da suke so.
Shugaban ya yi gargadin a guji amfani da kafafen sada zumunta wajen cin mutunci da tunzura jama’a.