Jam’iyyar NNPP ta bayyana cewa dan takararrata Rabiu Musa kwankwaso ya dauki Bishop Isaac Idahosa a matsayin wanda zai yi masa mataimaki a zaɓen shekarar 2023.

Cikin sanrwar da jam’iyyar ta fitar a twitter a yau Alhamis ta bayyana cewa ta zabi Isaac a matsayin mataimakin kwankwaso bisa nagartarsa.

Fasto Isacc dan asalin jihar Edo Babban fasto ne na coci mai suna Ilimunatiom Assembly Wanda ke lekki a jhar Legas.

Zabin na zuwa bayan rade radin da ake yi na cewa kwankwaso na neman tsohon gwaman jihar Anambra wato Peter Obi domin yi masa mataimaki.

A makon da mu ka yi bankwana da shi ne abokin hamayyar dan takarar jamiyar mai mulki wato Ahmad Bola Tinubu ya zabi tsohon gwamnan jjhar Borno Kashim Shettima a matsayin mataimakin shugaban kasa.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: