Hukumar kidaya a Najeriya ta nesanta kanta game da daukan ma’aikata da ake yadawa Hukumar zatayi.

Sanarwar ta fito ne daga mai magana da yawun hukumar kidaya ta kasa Isiaka Yahya.

Hukumar tana jan kunne da a kiyaye ga duk wanda yaga sanarwar daukan ma’aikata ba daga su bane damfarace.

Idan ba a manta ba a ranar 30 ga watan Mayun 2022 ne hukumar ta sanar ta dandalinta na sada zumunta da muhawara kan yadda wasu kafafen yada labarai na kasar suka bude hanyar daukar ma’aikatan wucin gadi don aikin ƙidayar gwaji a cikin ƙasa baki ɗaya.

Kwamitin ya yi fatan Nijeriya ta himmatu wajen tabbatar da gaskiya wajen gudanar da dukkan ayyukan da suka shafi gudanar da kidayar jama’a a shekarar 2023.

Leave a Reply

%d bloggers like this: