Gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawalle ya bayar da izini ga dukkan masarautun fadin Jihar da su nemi amincewar gwamnatin Jihar Kafin su nada wani sarauta a Jihar.

Babban mataimakin gwamnan a bangaren yada labarai Zailani Baffa shine ya fitar da sanarwar umarnin da gwamnan ya bayar.
Gwamnan ya bayyana cewa da sarakuna da hakimai manya da kanana na Jihar sai sun nemi yarjewa daga gwamnatin Jihar sannan za a nada wani rawanin sarauta.

Matawalle ya kara da cewa wannan doka da aka sanya an sanya ta ne domin sanya ido ga masu nadin sarauta ba tare da yin tunani ba wanda hakan ka iya zubar wa da masarautun Jihar kima.

Gwamna Matawalle ya ce dukkan wanda ya bijire wannan umarni da aka sanya za a dauki mataki akan sa.