Wasu “yan bindiga sun yi garkuwa da shanun fulani makiyaya “yan asalin Jihar Kebbi fiye da 2,000 a Jihar Sokoto.

Sakataren kungiyar Miyetti Allah a Jihar Kebbi Abubakar Bello Bandam shine ya bayyana hakan ga manema labarai, inda ya ce fulanin sun bayyana masa cewa ‘yan bindigan sun kwace musu shanun ne a safiyar ranar Laraba tare da kora su cikin dajin Jihar Zamfara.
“Yan bindigan sun tare fulanin ne a lkacin da su ke kan hanyar su ta komawa gidajen su da ke Jihar Kebbi.

Alhaji Abubakar ya kara da cewa a lokacin da makiyayan su ka hadu da “yan bindigan dauke da makamai hakan ya tilasta musu tsere wa su ka bar shanun na su.

Bayan tserewar makiyan “yan bindigan su ka kora shanun cikin dajin Jihar Zamfara.
Bandam ya ce ba tun yanzu ba makiyaya idan rani ya yi su na tafiya da dabbobin su kauyen Borgu domin kiwo daga bisani idan damina ta yi su koma gida.
Bello Bandam ya bayyana cewa ba a samu salwantar rayuka ba amma ba su da labarin halin da fulanin su ke ciki.
Sannan ya ce bayan faruwar lamarin sun shaidawa jami’an tsaro, inda ya ce yana da yakinin za su kuɓutar da shanun daga hannun “yan bindigan.
Sai dai yan sanda ba su ce komai ba a dangane da lamarin.