Kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta kara tsawaita yajin aikin da take da karin wasu makonni hudu domin baiwa gwamnatin tarayya karin lokaci domin biyan bukatun ta.

Kungiyar ta dauki matakin ne a karshen taronta na majalisar zartarwa ta kasa.

A wata sanarwa da shugaban kungiyar Farfesa Emmanuel Osodeke ya fitar, a ranar Lahadi kungiyar ta ce, byan tattaunawa mai zurfi tare da fahimtar gazawar gwamnati a baya wajen cika alkawuranta wajen magance matsalolin da suka taso a cikin yarjejeniyar tsakanin Gwamnatin tarayya da ASUU a 2020 (MOA), majalisar zartarwar ta yanke shawarar kara wa’adin yajin aikin zuwa wasu makonni hudu domin baiwa gwamnati karin lokaci don gamsuwa da warware dukkan batutuwan da suka rage.

Tsawaita yajin aikin ya fara ne bayan cimma matsaya da majalisar zartarwa na ƙungiyar su ka yi a jiya Lahadi.

Ƙungiyar malaman jami’a a Najeriya ASUU sun tsunduma yajin aiki ne fiye da watanni biyar da su ka gabata domin neman haƙƙoƙinsu a wajen gwamnati.

Leave a Reply

%d bloggers like this: