Kungiyar kiristoci ta Najeriya CAN a jihohin arewa 19 da Abuja, ta sake jaddada rashin amincewarta da tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC musulmi da musulmi.

Babban sakataren kungiyar Cristian Sunday Oibe, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a jihar Kaduna, watanni kadan gabanin zaben shugaban kasa.

Bayan nasarar da ya samu a zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar APC, Sanata Bola Tinubu – musulmi – ya bayyana Sanata Kashim Shettima a matsayin abokin takararsa a zabe mai zuwa.

Shettima, wanda ya taba zama gwamnan jihar Borno karo biyu, musulmi ne daga yankin arewa maso gabas, kuma dan majalisa mai wakiltar Borno ta tsakiya a majalisar dokokin tarayya da ke Abuja.

Shugaban kungiyar ta CAN ya kuma bayyana damuwarsa kan matsalar rashin tsaro da ke addabar sassan kasar nan, inda ya ce babu wanda zai tsira idan ‘yan ta’adda za su yi barazanar sace shugaban kasa da Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna.

Don haka ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya tashi tsaye wajen gudanar da wannan abu ta hanyar sauke nauyin da kundin tsarin mulki ya dora masa na kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa da kuma kare martabar Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: