Rahotanni daga jihar Gombe na tabbatar da cewar ambaliyar ruwan sama yayi sanadiyyar rasa rayuwar ƴar shekara uku sannan mai shekara biyu ya jikkata a Gombe.

Lamarin ya faru a garin Bajoga da ke ƙaramar hukumar Funakaye ta jihar Gombe.

Mamakon ruwan da aka yi na fiye da awanni biyar, wanda ya yi sanadiyyar rushewar wani ɗakin da yaran ke bacci a unguwar Fada kusa da fadar sarki.

Tuni aka kai wamda ya jikkata zuwa asibitin koyarwa na jihar domin kula da shi.

Yahaya Haruna ya bayyanawa jaridar Trust cewar an fara ruwan tun ƙarfe 05:30am na safe kuma aka yi shi da yawa har ƙarfe 11:00am na safe.

Ya ce sanadiyyar hakan an yi asarar dukiya mai dumbin yawa yayin da gidaje da dama su ka rushe.

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta SEMA ta tabbatar da faruwar lamarin, sai dai ta ce ta na ci gaba da tantancewa domin gano adadin gidajen da su ka ruahe da kuma asarar da aka yi.

A wani bayani da hukumar ta fitar, mai dauke da sa hannun mai magana da yawun hukumar Isma’il Uba, ya ce gwamnan jihar ya bayar da samar da hanyar rage raɗaɗi ga mutanen da iftila’in ya abka musu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: