Gwamnatin jihar Yobe ta raba kayan aikin gona ga manoma 500 na jihar.

Gwamnatin ta raba kayan ne ƙarƙashin hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Sema.
Babban sakatare a hukumar Dakta Mohammed Goje ne ya jagoranci raba kayan aikin gonar a ƙaramar hukumar Fune ta jihar.

Ya ce kayan tallafi ne daga shirin majalisar ɗinkin duniya na UNDP.

Sannan an horas da mutane 500 a kan yadda za su yi amfani da sinadrin kashe ƙwari da ake amfani da su a gona.
Mutanen sun hada da mata 100 maza 400.
Manoman sun rabauta da kayan aikin gona kamar iri, takin zamani, samar hannu, safar rufe baki da hanci da sauran sinadarin kashe ƙwari.