Wata babbar kotu da ke Jihar Akwa-Ibom ta yankewa wani basarake mazaunin Efam-Ibom da ke Jihar hukuncin kisa ta hanyar rayata sakamakon kamashi da aikata manyan laifuka.

Bayan gurfanar da basaraken a gaban kotun, an kamshi da hannu wajen hallaka wani mutum mai suna Udoma UdoUbom da kuma wasu manyan laifuka har guda hudu.
Alkalin Kotun Edem Akpan shi ne ya yanke masa hukuncin bayan kamashi da laifin yiwa wanda ya hallaka allurar guba tun a shekarar 2017 da ta gabata.

Udoma wanda basaraken ya hallaka ‘yan uwanshi ne su ka zarge shi da yin maita inda basaraken ya nemi da Udoma da ya rantse shi ba maye ba.

Bayan hukuncin da basaraken ya dauka ya tsere daga cikin kauyen inda jami’an tsaro su ka kamoshi tun a shekarar ta 2017.
Alkalin ya yanke hukuncin a lokacin da ya
kawo karshen shariar sakamakon kaifukan da aka wanda aka gurfanar a gaban kotun.